Wani direba mai shekara 55 ya tsira ba tare da rauni ba bayan wani jirgin ƙasa ya yi karo da motarsa a yankin PWD da ke jihar Legas ta Najeriya.
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, LASTMA, ta ce jirgin ƙasar na kan hanyarsa ta zuwa Agege lokacin da ya yi karo da motar Honda mai lambar rajista EKY 902 JT.
A cewar hukumar, motar ta samu mummunan lahani sakamakon haɗarin, duk da cewa ba a samu asarar rai ko jwani rauni ba.
LASTMA ta ce jami’anta, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro, sun taimaka wajen ceto direban da kuma cire motar daga kan layin dogo, abin da ya ba jirgin damar ci gaba da tafiyarsa.
Sai dai haɗarin ya haddasa cunkoson ababen hawa a yankin PWD.
An miƙa motar ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike kan musabbabin haɗarin.
Shugaban LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya yi kira ga direbobi da su riƙa taka-tsantsan a wuraren da hanyoyin mota ke tsallaka layukan dogo.
Ya kuma gargaɗe su da su guji ƙoƙarin tsallaka layin dogo idan jirgin ƙasa na gabatowa.
