Sufeton Janar na ‘Yan Sanda (IGP) ya naɗa CSP Anietie Okokon Edem Iniedu a matsayin sabon Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya.
CSP Anietie Iniedu ƙwararren jami’in ‘yan sanda ne mai gogewa a fannoni daban-daban kamar hulɗa da jama’a, aikin tsaro, tattara bayanan sirri da kuma harkokin gudanarwa a rundunar ‘yan sanda.
Kafin wannan naɗin, ya taɓa rike muƙamin Shugaban Sashen Karɓar Korafe-korafe a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja, inda ya kula da korafe-korafen jama’a da ƙoƙarin inganta gaskiya da amincewar jama’a ga rundunar.
Haka kuma, ya taɓa aiki a sassa daban-daban na ‘yan sanda ciki har da jihohi kamar Yobe da Abia, inda ya rike muƙamai daban-daban a fannonin aiki da tsaro.
Rundunar ‘yan sanda ta ce ana sa ran sabon kakakin zai ƙara inganta sadarwa tsakanin ‘yan sanda da jama’a, tare da tallafawa manufofin gyaran tsaro da ake aiwatarwa a ƙasar.
