- Aminu Abdullahi Ibrahim
Jimillar kudaden Harajin VAT da Najeriya ke samu sun ƙaru zuwa sama da tiriliyan 1.08 tiriliyan daya a watan Janairun 2026, yayin da sabon tsarin rabon kudaden VAT ya fara aiki, wanda ya sauya yadda ake raba kudaden tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
Takardun da aka gabatar a taron watan Fabrairu na na susun hadaka na gwamnatin tarayya (FAAC), sun nuna cewa hukumomin haraji sun tara VAT na N1.08 tiriliyan a Janairu 2026, idan aka kwatanta da biliyanm 913.96 da aka tara a Disambar 2025.
Ƙarin Naira biliyan 169.20 kenan aka samu, wanda ke wakiltar ƙaruwa da kashi 18.5 cikin 100 a wata-wata. Sai dai ba a raba duka N1.08 tiriliyan ba, domin an cire VAT da aka cire kai tsaye (deductions at source) har N79.94 biliyan a Janairu, daga N67.45 biliyan a Disamba. Hakan ya bar N1.00 tiriliyan a matsayin adadin VAT da za a raba.
A Disamba, adadin VAT da aka raba bayan cire-cire ya kai Naira biliyan 846.51. Don haka, an samu ƙarin naira biliyan 156.72 a Janairu, wanda shi ma ke nuna ƙaruwa da kashi 18.5 cikin 100.
Watan Janairu shi ne cikakken watan farko da aka fara amfani da sabon tsarin rabon VAT. A ƙarƙashin sabon tsarin, Gwamnatin Tarayya zata dauki kashi 10 cikin 100 na abunda aka tarayayinda jihohi zasu samu kashi 55 cikin 100, sai kashi 35 cikin 100 wanda za a rabawa ƙananan hukumomi.
A baya, Gwamnatin Tarayya na karɓar kashi 15 cikin 100, jihohi kashi 50 cikin 100, ƙananan hukumomi kuma kashi 35 cikin 100.
