Wasu ’yan asalin Jihar Kano biyu, Abba Ahmad da Lawal Haruna, mazauna Mazabar Durun da ke Ƙaramar Hukumar Kabo, sun rasa rayukansu a Jihar Legas, bayan wata hatsaniya da wasu mazauna yankin.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis 24 ga Satumba, 2026, a lokacin da matasan suke gudanar da harkokinsu na neman abinci a Jihar Legas, inda mutum guda kuma ya samu raunuka kuma aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
A wata hira da Premier Radio, tsohon Kansilan Durun, Honourable Yusuf Umar Durun, ya bayyana cewa rigima ce ta ɓarke tsakanin matasan da wasu ’yan asalin Legas, inda daga baya aka tara mutane aka kai musu farmaki, tare da amfani da makamai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Abba Ahmad da Lawal Haruna.
Ya ce an dauko gawarwakin mamatan daga Jihar Legas zuwa Kano, kuma a lokacin tattaunawar gawarwakin suna dab da isa Ƙaramar Hukumar Kabo domin a yi musu jana’iza.
Shi ma wani kawun ɗaya daga cikin mamatan Abdullahi Ali Durun, ya tabbatar wa Premier Radio cewa suna jiran isowar gawarwakin, domin yi musu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada kafin a yi jana’izarsu.
Da aka tambaye shi ko akwai wani mataki da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauka domin neman haƙƙin mamatan daga hannun gwamnatin Jihar Legas, ya ce bai da masaniyar wani mataki da aka ɗauka daga hukumomin Kano.
Sai dai ya ce shugabannin Hausawa da ke Jihar Legas sun yi alkawarin cewa za a tabbatar an yi wa iyalan mamatan adalci.
Ana sa ran yi wa Abba Ahmad da Lawal Haruna jana’iza a Mazabar Durun, Ƙaramar Hukumar Kabo, Jihar Kano.
