Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Daniel Bwala, ya bayyana cewa kafar yaɗa labarai ta Al Jazeera ta ba shi haƙuri a ɓoye kan wata hira da ya yi da ɗan jarida Mehdi Hasan, amma ta ƙi bayyana hakan a bainar jama’a.
Bwala ya ce abin da Al Jazeera ta bas hi hakuri a kai shi ne rashin sanar da shi tun farko cewa za a tambaye shi kan wasu kalamai da ya taɓa yi a baya dangane da Shugaba Bola Tinubu.
Ya ƙara da cewa bayan kafar ta ƙi fitar da wannan uzuri a fili, ya umarci lauyoyinsa da ke Birtaniya da su fara shigar da ƙara a kanta kan zargin ɓata masa suna.
Bwala ya kuma zargi Al Jazeera da yin gyaran bidiyon hirar ta hanyar rage tsawonta daga kusan awa ɗaya da rabi zuwa mintuna 49, inda ya ce an cire wasu muhimman sassa da suka nuna yadda ya mayar da martani ga tambayoyin da akayi masa.
