Bankin Duniya ya bayyana cewa kuɗaɗen shiga na jihohi 36 na Najeriya sun ƙaru da kashi 93 cikin ɗari tsakanin shekarar 2023 da 2025, sai dai kaso na kuɗaɗen da ake warewa fannin ilimi ya ragu.
A cikin sabon rahoton bankin kan ci gaban Najeriya, bankin ya ce kashe kuɗaɗen jihohin ma ya ƙaru da kashi 92 cikin ɗari a wannan lokaci.
Rahoton ya danganta ƙaruwar kuɗaɗen shiga da sauye-sauyen canjin kuɗi, cire tallafin man fetur, inganta tattara haraji da ƙarin rabon kuɗaɗe daga asusun tarayya.
Sai dai rahoton ya nuna cewa kaso na kuɗaɗen da jihohi ke warewa ilimi ya ragu daga kashi 14.9 a shekarar 2021 zuwa kashi 12.1 a shekarar 2025.
Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen da ake kashewa a fannin kiwon lafiya sun tsaya kusan kashi bakwai, yayin da kuɗaɗen tallafin jin daɗin jama’a suka ƙaru daga kashi 1.4 zuwa kashi 4.4.
Bankin ya kuma bayyana cewa, kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa sun ƙaru, inda suka kai kashi 61 cikin ɗari na jimillar kuɗaɗen da jihohi suka kashe, idan aka kwatanta da kashi 46 a baya. Fannonin sufuri da gine-ginen ababen more rayuwa ne suka fi samun ƙarin kuɗaɗe.
Daraktan Bankin Duniya mai kula da Najeriya, Mathew Verghis, ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga ya ba jihohi damar inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da samar da ruwan sha.
Sai dai ya jaddada buƙatar inganta yadda ake kashe kuɗaɗen jama’a, tabbatar da riƙon amana da kuma inganta ayyukan da jama’a ke amfana da su.
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da matsakaicin kashi 4.4 cikin ɗari a tsakanin shekarun 2026 da 2028, matuƙar aka ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da inganta ayyukan gwamnati.
Ya buƙaci gwamnatin tarayya da jihohi su tabbatar da cewa ƙarin kuɗaɗen shiga ya haifar da ingantuwar rayuwar ’yan Najeriya, musamman ta fuskar ilimi, kiwon lafiya da samar da ayyukan yi.
