Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Bankin Duniya da kada ya amince da sabon bashin dala miliyan 500 da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke neman karɓa, yana mai zargin gwamnatin da ƙoƙarin ɗora wa gwamnati mai zuwa nauyin biyan sabon bashi gab da sauka daga mulki.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta yaɗu ranar Talata, yayin da ake samun rahotannin cewa gwamnatin tarayya na shirin karɓar sabon rance daga bankin.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bai kamata gwamnatin da ke shirin barin mulki ta ɗauki sabon bashi wanda zai zama nauyi ga magajinta da kuma ’yan Najeriya ba.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da jinginar da makomar ƙasar, tare da kira ga Bankin Duniya da ya ƙi amincewa da buƙatar bashin.
Atiku ya ce: “Karɓar bashi kamar yadda mashayin giya ke yin abubuwa cikin rashin hankali, hanya ce ta shiga kangin tattalin arziki, wato wani nau’in bautar zamani. Idan wannan gwamnati ta ƙudiri aniyar jinginar da makomar Najeriya da kuma mayar da ƙasarmu ƙarƙashin ikon masu bin mu bashi, ba za mu amince da hakan ba.”
Ya kuma yi ikirarin cewa an tsara gabatar da buƙatar bashin dala miliyan 500 domin tantancewa a ranar 25 ga Mayun 2027, kwanaki huɗu kacal kafin rantsar da sabon shugaban ƙasa.
Atiku ya ce: “Shugaba Tinubu ba shi da wani dalilin ɗora wa ƙasar sabon bashi a daidai lokacin da yake shirin barin ofis.”
Ya ƙara da cewa: “Muna kira ga Bankin Duniya da kada ya amince da wannan bashin a lokacin da ake shirin gabatar da shi.”
Rahoton ya nuna cewa jimillar bashin da ake bin Najeriya a ƙasashen waje da cikin gida ya kai kusan naira tiriliyan 166.79 a watan Yunin 2026, bisa bayanan Ofishin Kula da Basussukan Ƙasa (DMO).
