Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn gurfanar da mutum 5 a gaban kotu kan cin naman mutum...

An gurfanar da mutum 5 a gaban kotu kan cin naman mutum a Zamfara

Date:

An gurfanar da wasu mutum biyar a gaban kotun majistare mai lamba daya a garin Gusau na Jihar Zamfara,  bisa zarginsu da kashewa tare da cin naman wani yaro.

PREMIER RADIO ta ruwaito tundunar yan sandan jihar ce ta gurfanar da mutanen ranar Talata.

Daga cikin wadanda aka gurfanar ɗin kuma ake zargi, har da wani fitaccen dilan motoci a Jihar.

Ana dai zarginsu ne da kashewa sannan suka ci naman wani Ahmad Yakubu Aliyu, wani yaro mai kimanin shekara tara a duniya.

Haka kuma an kai mutanen da ake zargi ne gaban kotun cikin tsauraran matakan tsaro.

Sai dai bayan da alkalin kotun, Mai Shari’a Sa’adu Gurbin Bore ya karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, sun musanta aikatawa.

Daga nan ne ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar takwas ga watan Fabrairun 2022 mai zuwa.

Iyayen yaron da sauran masu jajanta musu dai sun yi cincirindo a harabar kotun suna neman a hukunta wadanda ake zargin, inda suka ce lamarin abin takaici ne matuka.

Mahaifiyar yaron, wacce ta bayyana sunanta a matsayin Jamila Abdurrahman, ta shaida wa manema labarai cewa sun je kotun ne don bin kadin jinin dan nasu, da kuma tabbatar da cewa bai tafi a banza ba.

Daga nan ne sai alkalin kotun ya aike da mutum uku daga cikin wadanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali, yayin da ragowar biyun kuma ya aike da su gidan horar da kangararrun yara saboda karancin shekarunsu.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories