Ana danganta sunan Bauchi ne ga Malam Yakubu ɗan Dadi, wanda aka fi sani da Yakubu bin Dadi, almajirin Shehu Usman Ɗan Fodio.
A farkon ƙarni na 19, Shehu Usman Ɗan Fodio ya ba Yakubu bin Dadi tutar mulki, ya kuma aike shi zuwa yankin da ake kira Bauchi.
Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da aka kafa a Najeriya a ranar 3 ga watan Fabrairu, 1976, a lokacin mulkin soja Janar Murtala Muhammad, bayan raba tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas zuwa jihohi uku, wato Bauchi, Borno da Gongola.
A yau, jihar Bauchi na bikin cikar ta shekaru 50 da kafuwa, wani muhimmin lokaci da ke baiwa al’umma damar waiwaye, duba inda aka fito, inda ake, da kuma inda ake fatan zuwa nan gaba.
Tun kafuwarta, jihar ta kasance cibiyar tarihi da al’adu Bauchi na daga cikin jihohin da suka fi kowa yawan kabilu da harsuna a Najeriya, ciki har da Hausa, Fulani, Gerawa, Sayawa, Jarawa, Tangale inda take da ƙananan hukumomi guda ashirin, tare da al’ummomi daban-daban da ke rayuwa cikin zaman lafiya da juna.
Jihar Bauchi na da guraren tarihi kamar haka Yankari Game Reserve, mafi shahara kuma mafi girman gandun dajin kiwo a Arewacin Najeriya, Yankari na ɗauke da namun daji irinsu giwaye, barewa da sauransu, tare da ruwan zafi na Wikki Warm Spring, wanda ke jawo masu yawon buɗe ido daga ciki da wajen ƙasar.
A bangaren ilimi, Bauchi ta samar da manyan makarantu da dama ciki har da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa wacce ta kasance jami’ar fasaha ta farko a Arewa, kuma ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin koyar da kimiyya da fasaha a ƙasar nan.
A fannin Noma Jihar Bauchi ta kebanta da noman gero, dawa, masara, shinkafa da auduga, tare da kiwon shanu, awaki da tumaki abinda ya sanya ta zama ɗaya daga cikin manyan jihohin noma a Arewa.
Bauchi ita ce jihar da firaministan farko na Najeriya ya fito daga cikinta Sir Abubakar Tafawa Balewa, wanda sunansa ke ci gaba da haskakawa a tarihin ƙasar nan.
Haka zalika, jihar ta samu ci gaba a fannonin kiwon lafiya gine-ginen ababen more rayuwa, inda gwamnoni daban-daban suka bayar da gudummawa wajen shimfiɗa hanyoyi, gina asibitoci, da habaka harkokin noma, wanda shi ne ginshikin tattalin arzikin yawancin al’ummar jihar.
Sai dai duk da wadannan nasarori, jihar Bauchi na fuskantar kalubale da suka hada da talauci, rashin aikin yi, matsalolin tsaro a wasu yankuna, da kuma bukatar kara zuba jari a bangaren ilimi da lafiya.
Yayin da ake bikin cikar jihar shekaru 50, al’ummar Bauchi na kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki da su kara zage damtse wajen ciyar da jihar gaba, ta yadda shekaru masu zuwa za su zo da karin ci gaba da walwala ga al’umma.
Cikar jihar Bauchi shekaru hamsin ba wai bikin murna kawai ba ne, lokaci ne na tunani, tsari da kuma daukar sabbin matakai domin gina jihar da za ta dace da burin al’ummarta.
