Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaMuna aiki tare da ma’aikatar bunkasa ma’adinai a kokarinta na hada kai...

Muna aiki tare da ma’aikatar bunkasa ma’adinai a kokarinta na hada kai da bankin duniya domin samun rancen kudin da za a yi amfani dasu wajen ayyukan bunkasa bankaren hakar ma’adinai a kasar nan – Gwamnatin tarayya

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce tana aiki tare da ma’aikatar bunkasa ma’adinai a kokarinta na hada kai da bankin duniya domin samun rancen kudin da za a yi amfani dasu wajen ayyukan bunkasa bankaren hakar ma’adinai a kasar nan.

Wata sanarwar Segun Tomori, mataimakin musamman kan harkokin labarai na Ministan Ma’adinai Dele Alake, ta ruwaito ministan na fadin haka lokacin da daraktan bankin duniya anan Nijeriya Shubham Chaudhuri ya kai masa ziyara.

Mr Chaudhuri ya kuma bayyana gamsuwa dangane da kokarin farfado da ayyukan hakar ma’adinai da wannan sabuwar gwamnati ke yi, inda ya ce alamu sun nuna yadda Nijeriya ke shirin amfani da wannan bangare domin taiakawa habakar tattalin arzikin kasa.

Daraktan ya kuma jaddada shirin bankin duniyar na aiki are da gwamnatin tarayya domin samun kudin da za a yi amfani dasu musamman domin ayyuka a wasu sassan bangaren albarkatun ma’adinai.

Ministan Ma’adinai Dele Alake a nasa martani ya yaba da ziyarar jami’an bankin duniyar, tare da yaba yadda bankin ke taimakawa ci gaban tattalin arzikin kasar nan ta fannoni daban-daban a tsawon shekaru.

Latest stories

Related stories