Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa shirin yi wa ƙasa hidima (NYSC) domin ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da kyautata zamantakewa tsakanin al’ummomin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin rantsar da matasa masu yi wa ƙasa hidima na rukunin Batch C Stream I na shekarar 2026, a sansanin NYSC da ke Kusalla Dam, Ƙaramar Hukumar Karaye.
Abba Kabir, wanda Daraktan Ayyuka na Musamman, Alhaji Salisu Hassan Kofar Mata, ya wakilta, ya taya matasan murna, tare da bayyana shirin NYSC a matsayin muhimmiyar hanya ta haɗa kan ’yan Najeriya da fahimtar al’adu daban-daban.
Ya buƙaci matasan da su yi amfani da damar horon da ake ba su, wanda ya haɗa da koyarwa, atisayen soja, jagoranci, koyon sana’o’i da bunƙasa harkokin kasuwanci.
Haka kuma, ya buƙaci su kiyaye dokokin sansanin, su zama jakadu nagari da za su bayar da gudummawa wajen gina sabuwar Najeriya mai cike da kyakkyawan fata.
A nata jawabin, Babbar Jami’ar NYSC a Kano, Hajiya Halima A. Abubakar, ta bayyana cewa jimillar matasa 2,157, waɗanda suka ƙunshi maza 1,080 da mata 1,077, ne suka yi rajista domin halartar horon.
Ta kuma yabawa gwamnatin Kano, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bai
