Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari kan al’ummar Kasabo da ke Saminaka, ƙaramar hukumar Yauri a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin, inda ’yan bindigar suka shigo yankin da yawa, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin tserewa zuwa cikin daji domin tsira.
Wani mazaunin yankin, Aminu Salisu, ya ce maharan sun samu damar kashe mutum uku kafin su koma maboyarsu.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar yankin ranar Talata, inda ya bayyana harin a matsayin mummunan lamari da ba za’a amince da shi ba.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin ƙara haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da bayar da tallafin Naira miliyan 116 ga iyalan waɗanda aka kashe da sauran mutanen da harin ya shafa.
