Saurari premier Radio
33.4 C
Kano
Monday, September 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta samu nasarar kama wasu mutane da...

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zargin yiwa wani alkalin ma’aikatansa dukan kawo wuka

Date:

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta samu nasarar kama wasu mutum 5 da ake zargi da yi wa wani alkalin wata Kotu da ma’aikatansa 3 dukan kawo wuka a yankin Putuki da ke kauyen Degri na Karamar Hukumar Balanga ta jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Yammacin jiya Lahadin.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe Hayatu Usman, ya bada umurnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin domin bin diddigin binciken.
Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) reshen Jihar Gombe ta lashi takobin ganin an hukunta wadanda suka kai wa alkalin babbar kotun jihar tare da ma’aikatansa hari suka sassare su.
Shugaban kungiyar a jihar, Barista Benjamin Sati, ya ce muddin irin haka na faruwa da akalai da ma’aikatan kotu, to kasar nan babu wanda zai tsira.
Sanarwar da ya fitar bayan harin da aka kai wa alkalin da ma’aikatan nasa da aka yi wa duka aka sassare shi, ta nuna rashin jin dadinsu kan wadanda suka yi masa wannan danyen aiki.

Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne wasu bata-gari suka sassari alkalin wata Babbar Kotu ta III (UAC III) da ke Gombe, Ayuba Buba Dallas, da wasu ma’aikatan kotun uku a garin Degri da ke Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe.

Rahotanni sun ce sai da maharan suka yi wa alkalin da sauran mutane ukun dukan kawo wuka sannan suka sassare su.

Sauran wadanda lamarin ya shafa sun hada da wani lauya mai suna Barista Usman Yahya da wani ma’aikacin kotu.

Wata majiya ta ce wasu mutanen kauyen ne suka kai wa alkalin hari a lokacin da suke kokarin ganin sun warware matsalar rikicin wani fili.

Majiyar ta ce alkalin ya sha bugu ne daga kauyawan da ba a gane su ba a lokacin da shi da ma’aikatan kotun suka je duba filin a garin na Degri.

Wasu bayanai na alakanta harin da zargin da wasu ke wa ma’aikatan kotun da neman yin rashin adalci a takaddamar filin.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...