Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana aniyar fara sayen iskar gas daga Najeriya da nufin cike gibin makamashi da kasarsa ke fama shi tun bayan raba gari da Rasha sakamakon mamaye Ukraine da ta yi.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki daya kai lagos da Accra inda ya bayyana cewa gwamnatin jamus na shirin hada hannu wajen bullo da wata sabuwar hanya samun sinadarin hydrogen wanda ke samar da iskar gas.
Wannan shi ne karo na 3 da shugaban gwamnatin Jamus ke kai ziyara a kasashen Afirka a kokarin fadada alakar kasarsa tun bayan zama shugaban gwamnatin kasa da shekaru biyun da suka gabata.
Masana tattalin arziki naganin wannan wata hanya ce da zata karawa kasar nan hanyoyin kudin shiga da kimiya a siyasar duniya.