Saurari premier Radio
24.5 C
Kano
Sunday, September 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin jihar Kebbi ta raba kayan agaji ga mutane wadanda bala’in ambaliyar...

Gwamnatin jihar Kebbi ta raba kayan agaji ga mutane wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar a bara

Date:

Gwamnatin jihar Kebbi ta raba kayan agaji ga mutane 9,100 wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar a bara.
Jimillar mutane 22,202 ne za su gajiyar callafin daga kashi na farko da na biyu da kuma na uku.
Gwamna Nasir Idris a lokacin da yake jawabi a wajen raba tallafin kashi na farko ya sanar da kafa kwamitin da zai tabbatar da cewa kayayyakin sun isa ga wadanda aka yi niyya a kowace karamar hukumar jihar.
Gwamnan wanda mataimakinsa Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi ya wakilta ya ce kowane kwamiti zai kasance karkashin jagorancin kwamishina a karamar hukumar ko kuma mai ba shi shawara na musamman.
Tun da farko a nasa jawabin babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, Alhaji Mustapha Habib Ahmed wanda ya samu wakilcin Alhaji Ibrahim Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da daukar matakin musamman ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa bara.

Latest stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...