Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKarota ta kama mota makare da giya

Karota ta kama mota makare da giya

Date:

 

A karo na biyu ƙasa da mako guda, hukumar kula da Zirga-zirga Ababen hawa ta jiha Kano (KAROTA) ta ƙara kama mota ƙirar Tirela maƙare da Giya.

 

Ba jami’in mu ne ke shan giya a wani faifan bidiyo ba- KAROTA

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar a Alhamis din nan.

 

Hukumar ta sami nasarar kama Tirelar ne a kan titin Bello Dandago da misalin karfe 2:30 na daren Larabar da ta gabata, a ƙoƙarin su na shiga cikin Sabon Garin Kano.

 

Jami’an Hukumar ne suka kama motar a lokacin da suka buÆ™aci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya É—akko ta Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwali ya É—akko.

 

Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar.

 

Shugaban Hukumar KAROTA Hon Baffa Babba ÆŠan’agundi ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci garo da su wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba.

 

Ya Æ™ara da cewa za a Æ™ara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan domin ganin an daÆ™ile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta.

 

Ƙasa da sati guda hukumar ta cafke manyan motocin Tirela maÆ™are da Giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in (K40)da kuÉ—inta ya haura naira miliyan arba’in (N40m).

 

Da zarar an kammala bincike za a miƙa Giyar ga Hukumar Hizba domin ɗaukar mataki na gaba.
.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...