Gwamnatin tarayya ta fara shirin kwaso yan Najeriya dake zaune a Lebanon

0
71

Gwamnatin tarayya ta fara shirin kwaso yan Najriya dake zaune a Lebanon biyo bayan ta’azzarar rikici tsakanin isra’ila da Iran.

Mataimakawa shugaban kasa akan kafoffin sada zumunta, Dada Olesegun ne ya bayyana haka a shafinsa na X. inda ya bukaci yan kasa su hanzarta shigar da bayanan su a ofoshin jakadancin Najeriya dake Lebanon.

Akalla yan Najeriya dubu biyar ne ke zaune a Lebanon a halin yanzu.

A ranar Talatar nan Iran ta harba makamai masu linzami 180 akan israila a matsayin martini kan harin da israilar takaiwa shugaban Hezbollah.

Tuni aka jiyo fara ministan Israila Benjamin Netantahu, na shan alwashin mayar da tsatsauran martini akan Iran duk da sanya bakin da kasashen China da Saudi arabia sukayi don samun masalaha a wannan rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!