Hukumar NITDA ta zaɓi mata ‘yan kasuwa 317 domin shiga zagaye na uku na shirin IgniteHER, wanda aka ƙirƙira domin taimaka wa mata wajen amfani da fasahar zamani da kuma samun damar jawo masu zuba jari.
Darakta Janar na hukumar, Malam Kashifu Inuwa, ya ce ana gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar hukumar JICA ta ƙasar Japan, inda mahalarta za su samu horo kan ƙirƙire-ƙirƙire, dabarun kasuwanci da hanyoyin samun jari.
A zagaye biyu da suka gabata, mata 220 ne suka samu horo. Hukumar ta ce wata daga cikin tsofaffin mahalarta ta samu jarin dala dubu 500, bayan cin gajiyar damar da shirin ya samar.
An kafa cibiyoyin shirin a jihohin Kano, Jigawa, Rivers da Enugu, yayin da NITDA ke shirin faɗaɗa shi zuwa dukkan jihohin Naje
