Gwamnatin Kano ta musanta wani rahoto da kungiyar Tracka ta fitar, wanda ya zargi gwamnatin da ware fiye da Naira miliyan 235 a kasafin kudin shekarar 2025, domin gina azuzuwa a wata makarantar sakandaren ’yan mata dake garin Massu a karamar hukumar Sumaila.
Kwamishinan yada labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda ya ce zargin ba shi da tushe, kuma babu wata shaida da ke nuna an biya kudin a rahoton aiwatar da kasafin kudin jihar na zangon karshe na 2025.
Waiya ya ce kasafin kudin jihar Kano na 2025 ya kai Naira biliyan 719 da miliyan 557, inda aka ware Naira biliyan 168 da miliyan 350 ga bangaren ilimi, wanda ya haɗa da kudaden gyaran makarantu, daukar malamai, samar da kayan makaranta da tsaro, da kuma gudanar da manyan ayyukan ilimi a kananan hukumomi 44.
Kwamishinan ya ce babu wani aiki mai suna GGSSS Massu, Sumaila na fiye da Naira miliyan 235 a kasafin kudin 2025 ko takardun amincewar majalisar zartarwar Kano akan hakan, kuma dukkan ayyukan gwamnati ana tantance su tare da bin ka’idojin da suka dace kafin gudanarwa, inda ya ce yanzu haka Ma’aikatar Ilimi da hukumar SUBEB na gudanar da bincike kan ayyukan ilimi a Sumaila, kuma za’a bayyana sakamakon binciken ga jama’a.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya Kwamishina Waiya na kalubalantar ƙungiyar ta Tracka da sauran kungiyoyin fararen hula da su gabatar da shafin kasafin kudin da lambar aikin da suka dogara da ita, da kuma shaidar bayar da kwangila, biyan kudi, sunan dan kwangila da bayanan ziyarar bincike da suka ce sun gudanar a Massu.
