Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga waɗanda suka tsira da kuma iyalan waɗanda aka kashe a kisan Asaba da su rungumi yafiya da sulhu, yayin da ake bikin cikar shekaru 59 da faruwar lamarin.
Obasanjo ya yi wannan kiran ne a ranar laraba, yayin da ya halarci bikin tunawa da kisan Asaba ta kafar sadarwa, inda ya kasance shugaban taron, ya bayyana kisan a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi muni da raɗaɗi da suka faru a lokacin yaƙin basasar Najeriya.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce ya zubar da hawaye bayan da ya karanta wasu takardu da suka shafi kisan da aka liƙa masa, yana mai cewa abin ya ba shi matuƙar damuwa ganin irin wannan lamari ya faru a Najeriya a lokacin da yake raye, ya kuma jaddada muhimmancin tunawa da lamarin domin kauce wa sake faruwar irin sa.
Sai dai Asagban Asaba, Obi Epiphany Azinge, ya ce yafiya ba tana nufin mantawa da abin da ya faru ko watsi da buƙatar ayi adalci ba, ya kuma bayyana cewa al’ummar Asaba sun yafe wa iyalan kanal Ibrahim Taiwo, wanda ake danganta shi da aikin soji a lokacin kisan, bayan ɗansa, mai ritaya manjo janar Ahmed Taiwo, ya gabatar da uzuri da neman afuwa.
Asagban ya ƙara da cewa har yanzu al’ummar Asaba na neman shugaban kasa mai ci ya ba su haƙuri a hukumance kafin su samu cikakken kwanciyar hankali da rufe wannan babin, rahotanni sun ce kisan Asaba ya faru ne tsakanin ranakun 5 zuwa 7 ga Oktoban 1967, a lokacin yaƙin basasar Najeriya.
