Shugabar Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Jihar Kano (ALGON) kuma Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada, Sa’adatu Yusha’u Soja, ta tsallake rijiya da baya bayan da wasu da ake zargin ɓatagari ne suka kai hari kan tawagarta bayan kammala taron tabbatar da ɗan takarar Sanatan Kano ta Kudu na jam’iyyar APC a garin Rano.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da tawagar shugabar ke dawowa daga taron siyasar, inda maharan suka farmaki motar da take ciki tare da lalata wasu sassa na motar kafin jami’an tsaro su samu nasarar fitar da ita cikin aminci.
Hotunan da suka bayyana bayan harin sun nuna yadda motar ta lalace sakamakon harin, lamarin da ya janyo fargaba tsakanin magoya baya da mazauna yankin.
