Wata yar majalisar dokoki ta jihar Florida a Amurka, Kimberly Daniels, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta cire ko ta sauya Bello Matawalle daga mukaminsa na karamin ministan tsaro.
Kimberly Daniels ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026 yayin gabatar da wani rahoto kan matsalar tsaro a Najeriya.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa rahoton da aka gabatar ya fi mayar da hankali a kan kashe-kashen da aka samu a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
Rahoton ya yi nazari kan yadda shugabancin tsaro ke aiki, musamman bayan hare-haren da suka faru a lokacin bukukuwan Easter na shekarar 2026.
Ta ce shugabannin al’umma da wadanda suka tsira sun koka da cewa akwai babban gibi tsakanin kalaman gwamnati da ainihin halin tsaro a kasa kamar yadda ya ke shafar su.
Rahoton ya kuma nuna damuwa kan ci gaba da rike mukamin ministan tsaro da Bello Matawalle ke yi inda aka ambaci wasu “alamun gargadi”, ciki har da zargin alaka da yan bindiga a lokacin da yake gwamnan Zamfara.
Kimberly Daniels ta ce an kuma zargi Matawalle da boye shugabannin yan bindiga da kuma rashin gogewa a harkar tsaro.
