
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar dake tabbatar da daidaito wajen aiwatar da allurar rigakafi a jihar wato Kano Community of Practice (CoP) da kungiyar Save the Children sun bayar da horo kan hanyoyin da za a bi domin inganta allurar rigakafi.
An gudanar da taron ne karkashin shirin Boost wanda Save the Children International ke aiwatarwa tare da tallafi daga GlaxoSmithKline (GSK), don haɓaka dabarun da suka dace domin rage yawan adadin yaran da basa samun allurar rigakafi a yankin Ungoggo da Gezawa.
Da yake jawabi manajan shirin na BOOST Abdullahi Ibrahim Magama, ya ce shirin ya mayar da hankali ne kan gano gibin da ke akwai da kuma ƙarfafa ƙoƙarin bayar da shawarwari don inganta rigakafi.
Magama, ya bayyana cewa aikin, wanda aka fara aiwatarwa a watan Janairun 2024 kuma ana sa ran zai ci gaba har zuwa Disambar 2027, tare da tabbatar da an samu karuwar yaran da ake yiwa rigakafi a kananan hukumomin Gezawa da Ungogo.
Ya jaddada bukatar kara kudin da gwamnati ke warewa rigakafi domin wayar da kai tare da zuwa kauyukan da basu da asibitoci don yi musu.

Ya ce hukumomi su shigo don tallafawa ma’aikata da kayan aikin da ake buƙata tare da basu isashen kulawa.
Cutar shan Inna ta sake bulla a Jihar Zamfara
Jami’in wayar da kai na shirin Boost, Umar Ibrahim, ya yi kira ga membobin kwamitin na (CoP) da su ci gaba da jajircewa wajen cimma nasarar shirin.
A nasa bangaren, Shugaban Kano Community of Practice (CoP) Salisu Yusuf, ya ce sun duba wani kundi mai dauke da bayanai nay aa da kananan hukumomin da yara basu samu rigakafi ba.
Ya ce sun fitar da tsare-tsare na kai ziyara yankunan Ungoggo da Gezawa wanda bincike ya nuna cewa a jihar Kano suna fama da karancin yara da aka yiwa allurar rigakafi.

Salisu Yusuf, ya kuma ce zasu kai ziyara ga kwamishinan lafiya da majalisar dokokin Kano domin lalubo hanyoyin da za a inganta fitar da kudi domin allurar rigakafi a jihar Kano.
Yusuf ya ƙara da cewa babban burin shine a tabbatar da cewa matsalar yara marasa allurar riga-kafi ta ragu sosai a faɗin jihar Kano.
