
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shirin dake inganta kiwo na bankin duniya hadin gwiwa da gwamnatin Kano (L-PRESS) zai samar da rijiyoyin burtsatse da ciyawa a guraren manoma domin magance matsalar rikicin Fulani makiyaya da manoma.
Ko-odinetan shirin a nan Kano Salisu Muhammad Inuwa ne ya bayyana haka yayin taron tsakiyar shekara na duba aikace-aikacen shirin a jihohi bakwai da aka gudanar ranar Litinin.
Ya ce suna da shirin samar da mayankar Abatuwa ta zamani wacce za ta ingata fitar da nama daga jihar Kano zuwa kasashen ketare.
CITAD Ta Tallafa wa Yara 100 da Tufafi da Kayan Karatu a Makarantar Nomadic Ta Fulani a Kano
Salisu Muhammad Inuwa ya ce suna da manufar shigo da sabon iri ta yadda dabbobin da ake da su za su rinka bayar da madara mai yawan da ake bukata.
Kodinetan shirin na L-PRESS a nan Kano Salisu Muhammad Inuwa, ya kuma ce a taron tsakiyar shekaran za su duba nasarori da kalubale tare da fito da hanyoyin inganta shirin.
