Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta rahoton da ke zargin cewa an yi masa tayin Naira biliyan 500 ko kuma yana da hannu a wani shiri na raba ƙuri’un yankin Kudu Maso Kudu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Jonathan ya bayyana rahoton a matsayin na ƙarya marar tushe, tare da yin kira ga ’yan kasa da su yi watsi da shi.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dakta Ikechukwu Eze, ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce rahoton ƙagaggen labari ne da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a da kuma jefa tsohon shugaban ƙasar cikin cece-kuce na siyasa.
Ya jaddada cewa Jonathan bai taɓa halartar wani taro ko shiga wata tattaunawa ko yarjejeniya da ta shafi wannan zargi ba.
Eze ya bayyana cewa tun bayan barin mulki a shekarar 2015, Jonathan ya ci gaba da kasancewa jagoran ƙasa mai mutunta dimokuraɗiyya, inda yake inganta zaman lafiya, shugabanci nagari da ingantaccen tsarin dimokuraɗiyyar a Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika.
