Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Najeriya, tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Ɗaliban Jami’o’i ta Ƙasa (NAUS), ta ƙaddamar da gasar shirya bidiyo da za a raba kyaututtukan kuɗi na naira miliyan 4.4 ga waɗanda suka yi nasara.
Gasar mai taken #SecureTheGrid na da nufin wayar da kan jama’a game da muhimmancin kare kayayyakin wutar lantarki daga sata da lalata su, waɗanda ke kawo cikas ga samar da wutar lantarki a ƙasar.
A tsarin gasar, ɗalibin da ya lashe matsayi na farko zai samu naira miliyan ɗaya, tare da ƙarin dubu ɗari biyar ga gwamnatin ɗaliban jami’arsa.
Wanda ya zo na biyu zai samu naira dubu ɗari biyar, na uku kuma naira dubu ɗari biyu, yayin da wasu ɗalibai 12 za su samu naira dubu ɗari ɗaya kowannensu.
Domin shiga gasar, ana buƙatar ɗalibai su shirya bidiyo mai tsawon daƙiƙa 45 zuwa 60, sannan su wallafa shi a shafukan sada zumunta na TikTok, Facebook, Instagram ko X.
Dole ne bidiyon ya ƙunshi sunan ɗalibi da jami’arsa, tare da amfani da alamomin #SecureTheGrid da #ProtectPowerAssets.
An saka ranar 30 ga Nuwamba, 2026, a matsayin ranar ƙarshe ta karɓar bidiyoyin, inda za a tantance waɗanda suka yi nasara bisa yawan mu’amalar da bidiyoyinsu suka samu a shafukan sada zumunta.
