Gwamnatin Kano ta yi turr da kalaman da tsohon Mataimakin Gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi, inda ya zargi gwamnatin da yin watsi da mutanen da gobara da ambaliyar ruwa suka shafa a sassan jihar.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa da kare afkuwar Ibtila’i na Kano, Isyaku Abdullahi Kubaraci, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce zargin ba shi da tushe balle makama.
Kubaraci ya ce kalaman na Gwarzo cike suke da san zuciya wadanda suke ƙara fito da irin mummunar rawar da ya taka lokacin da yake mataimakin gwamna, musamman a ɓangaren bukatar sa na son a sakar masa hakkin al’ummar Kano yayi abinda ya ga dama da su.
Isyaku Kuburaci ya ce gwamnatin Kano ta dauki matakai da dama wajen kai dauki ga wadanda ibtila’o’i suka shafa, tare da jaddada cewa ana ci gaba da tallafawa al’ummomin da gobara da ambaliyar ruwa suka shafa a fadin jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kubaraci na buƙatar al’umma da su yi watsi da dukkan kalaman da ka iya haifar da rudani, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da cika nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma tallafawa wadanda suka fuskanci ibtila’i.
