Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 30 ga Oktoban 2026.
Ya ce shirin, mai suna NERSI, zai tallafa wa gidajen da ke fama da matsin tattalin arziki, inda za a zaɓi waɗanda za su amfana ta hanyar rajistar talakawa ta ƙasa.
A cewarsa, waɗanda aka zaɓa za su samu saƙon SMS domin tabbatar da amincewarsu kafin a tura musu kuɗin ta asusun banki ko walat ɗin waya.
Ministan ya jaddada cewa tallafin kyauta ne, kuma ba a buƙatar cike sabon fom ko biyan kuɗin rajista.
Ya kuma gargaɗi jama’a da su yi hattara da masu zamba, tare da guje wa bayyana lambobin sirrin asusun bankinsu.
