Mai sharhi kan harkokin siyasa, Mahdi Shehu, ya yi gargaɗin cewa tabarbarewar tsaro a Najeriya, musamman a jihohin Arewa, na iya kawo cikas ga gudanar da babban zaɓen 2027.
A wata hira da jaridar Daily Post, Shehu ya ce hare-haren ’yan bindiga, ƙauracewar jama’a daga muhallansu, talauci da raguwar sha’awar zaɓe na iya hana miliyoyin ’yan Najeriya kaɗa ƙuri’a.
Ya ambaci jihohin Borno, Yobe, Katsina, Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi a matsayin yankunan da matsalolin tsaro suka daɗe suna addaba.
Shehu ya kuma yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki na iya cin gajiyar matsalar tsaron idan aka yi amfani da ita wajen ayyana dokar ta-ɓaci maimakon gudanar da zaɓe.
