Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga neman tikitin tazarcen kujerar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC, gabanin zaɓen fidda gwani da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis.
Fubara ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai taken “My Decision to Withdraw from the Rivers State Gubernatorial Primaries”, wadda ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba.
A cikin sanarwar da jaridar Daily Trust ta gani, Gwamnan ya ce ya yanke shawarar janye takararsa ne bayan yin nazari mai zurfi kan yanayin siyasa da kuma muradun jam’iyyar.
Sai dai ya tabbatar da cewa zai marawa duk wanda ya samu tikitin takarar Gwamna na jam’iyyar APC baya domin tabbatar da haɗin kai da nasarar jam’iyyar a zaɓen da ke tafe.
