Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki buƙatar shugaba Bola Tinubu ga majalisar dokoki ta kasa na neman amincewa da sabon bashin waje.
Buƙatar ta ƙunshi bashin dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.05.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da rashin bayar da cikakken bayani kan ayyukan da za a kashe kuɗaɗen a kansu, da wuraren da za a gudanar da su da kuma yadda za a biya bashin.
Atiku ya buƙaci Majalisar Tarayya kada ta amince da buƙatar har sai gwamnati ta bayyana cikakkun bayanan ayyukan da bashin zai ɗauki nauyi.
Atiku ya nuna rashin amincewarsa da wannan mataki, yayin da ake ci gaba da muhawara kan yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da bashin ƙasar.
