Gwamnatin Kano ta ce kawo yanzu fiye da masu larurar amsanin jini (Sickler) dubu 13 ne ke amfanar tsarin ta na kula da lafiyar su kyauta, a karkashin shirin nan na Abba Care da ta bullo da shi domin tallafar rayuwar su.
Shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta Kano Dr Rahila Mukhtar ce ta bayyana hakan, yayin tattakin da hukumar ta shirya a wani bangare na bikin ranar masu ciwon amosanin jinin ta duniya.
Dr Rahila ta ce larurar ta amosanin jini cuta ce wadda take da matukar cin kudi da bukatar ingantacciyar kulawa akai-akai, hakan ce ta sanya gwamna Abba Kabir Yusuf ya samar da tsarin na Abba Care domin kula da lafiyar kyauta a fadin Kano.
Dr Rahila ta ce daga cikin yunkurin da gwamnatin Kano take yi na takaita yaduwar cutar ne, yasa aka samar da dokar yin gwajin lafiya kafin aure domin gujewa haihuwa ‘ya’ ya masu cutar da gujewa fadawa matsalolin da masu ita suke fuskanta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Rahila na bukatar iyaye da su dinga daukar matakin yin gwajin lafiya da wuri kafin ‘yar su ta saba da wanda ya zo neman auren domin gujewa fadawa tarkon da na sani.
