Hukumar Ƙididdiga Ta Najeriya (NBS) ta ce, arzikin da Najeriya ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ƙaru da kashi 3.98 cikin 100 a rubu’i na uku na shekarar 2025.
Cikin rahoton da hukumar ta fitar, ta ce arzikin cikin gida da Najeriya ta samu a watannin rubu’i na uku na shekarar ya zarta wanda ta samu a daidai wannan lokacin na shekarar 2024.
Talauci ne tushen matsalolin dake addabar Arewacin Najeriya – Gwamnan Jigawa
NBS ta ce fannin noma ne kan gaba a samar da arzikin da kashi 3.79 sai harkar masana’antu da ya ƙaru da kashi 3.77.
A baya-bayan ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, kamar yadda hukumar ta NBS ke fitarwa, wani abu da gwamnatin ƙasar ke dangantawa da matakan inganta tattalin arziki da take ɗauka.
take ɗauka.
