Ɗan takarar jam’iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya samu nasara a zaɓen kujerar Sanatan Jihar Michigan ta Amurka, inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar Republican, Mike Rogers.
Tashoshin CNN, CBS da NBC sun bayyana El-Sayed a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan samun rinjaye yayin ƙidayar ƙuri’u.
Bisa alkaluman da CNN ta bayyana bayan ƙirga kashi 93 cikin 100 na ƙuri’un, El-Sayed ya samu kashi 52.2, yayin da Rogers ya samu kashi 45.8.
El-Sayed, mai shekara 42 kuma tsohon jami’in kula da lafiyar jama’a, ya zama Musulmi na farko da aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Amurka.
Nasararsa ta zo ne duk da rikicin siyasar da ya biyo bayan matakin ƴar Majalisar Wakilai, Haley Stevens, wadda ya kayar a zaɓen fidda gwani na Democrat, na marawa abokin hamayyarsa Mike Rogers baya kwanaki kaɗan kafin zaɓen.
