Ministan Kudi Wale Edun ya bayyana cewa Najeriya ta samu kudaden shiga da suka kai naira tiriliyan 6.9 a cikin watanni ukun farko na shekarar 2025.
Edun ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin wani taron tuntuba da wayar da kai tsakanin gwamnati da ‘yan kasa da masu ruwa da tsaki, dangane da aiwatar da manyan manufofin Shugaba Bola Tinubu, wanda aka gudanar a birnin Abuja.
Ministan ya ce, wannan adadi ya nuna karin kaso 40 cikin 100 idan aka kwatanta da naira tiriliyan 5.2 da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar da ta gabata.
Ya kuma kara da cewa karin kudaden ya biyo bayan wasu sauye-sauye da aka samu kwanan nan, musamman wadanda suka shafi musayar kudade.
