Majalisar dokokin jihar Kano tace ta janye tuhume tuhumen da take yiwa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo biyo bayan ajiye mukamin sa na Mataimakin Gwamna Jahar Kano
Majalisar ta bayyana hakan ne a zaman ta na yau karkashin Jagorancin Rt Hon Jibrin Isma’il Falgore.
Da yake Karin haske dangane da lamarin, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Hon Lawan Husaini Cediyar Yan’gurasa yace , Yanzu majalisar bata da wani hurumi akan batun tuhumar da take yiwa tsohon mataimakin gwamnan
“Dama iya hurumin mu shi ne muyi bincike idan an same shi da laifi mu tsige shi daga mukamin sa. to sai gashi ya sauka tun kafin ma mu kammala, don haka yanzu bamu da wani hurumi tun da mu ba yan sanda ba ne”
Kazalika majalisar ta Amince da ritayar Mataimakin Gwamna a hukumance, waliyarmu Binta Khalid Mohd ta rawaito cewa a yayin zaman majalisar na yau dan’majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kiru Hon Usman Tasi’u ya sanarwa da majalisar cewa ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa ADC
