Rundunar ‘yansanda ta kasa ta kama wasu mutane da ke sayar wa ‘yan bindiga da mayaƙan Boko Haram babura a jihohin Neja da Kaduna.
Mataimakin Babban Sufeto-Janar na ‘yansanda mai kula da Shiyya ta Bakwai, Benneth Igweh ne, ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata.
An kama wadanda ake zargi Shamsuddeen Yunusa mai shekara 30, da Zaharadeen Saidu mai shekara 25, da kuma Mustapha Haruna mai shekara 22 a garin Suleja dake Jihar Neja.
“Wadannan mutane sun ƙware wajen satar babura da sayar da su ko bayar da haya ga ‘yan ta’adda da ke jihar Neja da kuma yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna”. Inji shi
Mista Igweh ya kuma ce, sun samu babura 22 da makullai da dama da wayoyin hannu a hannun waɗanda ake zargi.