
Aminu Abdullahi Ibrahim
Jihar Kano na gab da samun katafariyar cibiyar kula da harkokin kiwo irinta ta farko a arewacin kasar nan da zata rinka fitar da madara da nama zuwa kasashen ketare.
Tuni dai aiki yayi nisa wajen gina wannan muhimmiyar cibiya a Bagauda dake karamar hukumar Bebeji wacce ake sa ran zata bunkasa tattalin arziki da samar da aikin yi.

Shirin inganta kiwo (L-Pres) na bankin duniya da hadin gwiwa da gwamnatin Kano ke samar da masana’antar wacce ta kunshi gurin kiwo na zamani, gurin samar da madara da babbar mayanka ta zamani.
INEC ta ce jam’iyyun ADC, PDP da LP ba za su shiga zaben cike gurbi ba a Jihar Rivers.
Da yake jawabi ko-odinetan shirin na kasa Sanusi Abubakar, yayin duba wasu aiyukan da shirin (L-Pres) ya aiwatar a nan Kano ya ce tuni aka ci kaso 30 na gina babbar cibiyar kuma ana sa ran kamala aikin zuwa karshen shekarar da muke ciki.

Ya ce shirin yana aiki tare da hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kano domin janyo wadanda zasu zuba jari tare da tabbatar da cewa manoma masu kiwo suna amfana da masana’antar.
Dangane da kula da cibiyar Sunusi Abubakar, ya ce al’umma ne zasu dauki gabaran kula da ita ta hanyar gudanar da harkokin kasuwanci yayin da gwamnati zata taka rawa gina tituna da ofishoshin gudanarwa da tsaro.
Baya ga wannan muhimmin aiki shirin (L-PRES) ya samar da babban gurin sarrafa madarar shanu a Dan Tuben Fulani da Gamu a karamar hukumar Dawakin Kudu.
Da yake jawabi ko-odinetan shirin a nan Kano Salisu Muhammad Inuwa, ya bayyana taron tsakiyar shekara da suka gudanar a matsayin hanyar da zata taimaka wajen duba nasara da kalubalan da suka fuskanta a shekaru 3 da suka gabata.

Ya kuma nuna gamsuwa bisa irin nasarorin da aka samu na gabatar da manyan aikace-aikace a jihar Kano.
Gambo Abubakar daya ne daga cikin wadanda suka amfana da injin sarafa kara da samar da abincin dabbobi a garin Dan Tuben Fulani a karamar Hukumar Dawakin Kudu, ya ce shirin ya inganta yadda suke ciyar da dabbobinsu tare da magance matsalolin da suke fuskanta a yankinsu.
L-Pres ta jagoranci sansanta rikicin Fulani Makiyaya da Hausa Manoma a karamar hukumar Takai.
Itama Aisha Abubakar Muhammad, daga yankin Gamu a Dawakin Kudu ta bayyana yadda tallafin da suka samu daga L-PRES ta hanyar kungiyar su mai suna Dairy Cooperative Union ya canza musu rayuwa.
Ta ce sun samu tallafin na’urar lantarki mai amfani da hasken rana da Burtsatse da abin hawa da Injinan sarrafa nono zuwa na zamani.
Ta ce a baya basa iya kai ‘ya’yansu makaranta amma lamarin ya canza a yanzu bayan samun tallafi na dogaro da kai daga shirin na L-Pres.
Shirin na L-Pres zai cigaba da aiwatar da aikace-aikace da samar da tallafi a bangarori daban daban domin inganta harkokin kiwo a jihar Kano da kasa baki daya.
