Jam’iyyar PDP da magoya bayan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a Jihar Gombe sun nuna damuwa kan rashin sanya sunansa cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamna da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar.
A cikin wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya fitar a daren jiya, ya bayyana cewa rashin sanya sunan Pantami na da alaƙa da zaɓen fidda gwani da aka sake gudanarwa a ranar 29 ga Satumba, 2026, bisa umarnin Babbar Kotun Tarayya.
Sanarwar ta buƙaci mambobin jam’iyyar PDP da magoya bayan ƙungiyar Pantamiyya da su kwantar da hankulansu, tare da ci gaba da kasancewa masu kyakkyawan fata, tana mai cewa matsalar ba hukunci na ƙarshe ba ne.
Farfesa Suleiman ya ƙara da cewa tawagogin lauyoyinsu da masu hulɗa da hukumomi sun fara tattaunawa da shugabannin PDP da hukumar INEC domin ganin an shawo kan matsalar tare da bin ƙa’idojin da doka ta tanada.
Ya kuma nuna fatan cewa za a warware matsalar domin tabbatar da cewa an bi dukkan matakan da suka dace.
