Wani ɗan kwangila ya shaida wa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja yadda ya tura naira miliyan shida zuwa asusun matar tsohon shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT), Danladi Umar, tare da biyan kuɗin karatun ’ya’yansa biyu a jami’a.
Ɗan kwangilar, Oluwatayo Fashogbon, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bayar da shaida a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar kan Danladi Umar.
Fashogbon, wanda ke shugabantar kamfanonin Portal Realities Limited da JTF Global Links Limited, ya ce tsohon shugaban CCT ya buƙace shi da ya tura naira miliyan shida zuwa asusun matarsa, Zulaihatu Danladi Umar, a ranar 25 ga Janairun 2024.
A cewarsa, buƙatar ta zo ne kwanaki biyu bayan kamfaninsa ya karɓi wani kaso na kuɗin kwangilar da CCT ta ba shi.
Ya bayyana cewa kwangilar, wadda darajarta ta kai kusan naira miliyan 140, ta shafi mayar da bayanan ma’aikata da wasu ayyukan hukumar zuwa tsarin zamani na kwamfuta.
Shaidan ya kuma ce an buƙace shi da ya biya kuɗin karatun ’ya’yan Danladi Umar biyu a Jami’ar Baze da ke Abuja, inda ya biya kusan naira miliyan biyu ga ɗaya daga cikinsu tare da yin makamancin wannan biyan ga ɗayar.
Yayin da lauyan EFCC, Christopher Mshelia, ke jagorantar bayar da shaidarsa, Fashogbon ya gabatar da takardar bayar da kwangilar, wadda kotun ta karɓa a matsayin hujja.
Sai dai yayin amsa tambayoyin lauyan wanda ake tuhuma, ɗan kwangilar ya tabbatar cewa kamfaninsa na da cancantar gudanar da kwangilolin gwamnati.
EFCC na tuhumar Danladi Umar da laifuka huɗu da suka shafi zargin amfani da matsayinsa wajen samun wata fa’ida ta kuɗi da ta kai naira miliyan 15.59.
Danladi Umar ya musanta zarge-zargen da ake masa.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairun 2027.
