Sama da ’yan Najeriya 3,000 da suka dawo daga Saudiyya sun kasance ba tare da kayansu ba, bayan wani cikas da ya shafi jigilar kayayyakin fasinjoji da kamfanin jirgin Saudi Airlines ya samu.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NCAA, ta ce kimanin tan 180 na kayan fasinjojin har yanzu suna makale a birnin Jeddah na Saudiyya.
Daraktan sashen kare haƙƙin fasinjoji da hulɗa da jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ya bayyana cewa hukumar ta shiga tsakani a makon da ya gabata, lamarin da ya sa aka dawo da kusan tan takwas na kayan zuwa Najeriya.
Sai dai Achimugu ya ce wannan adadin ƙalilan ne idan aka kwatanta da yawan kayan da har yanzu suke Jeddah, domin sama da fasinjoji 3,000 ne matsalar ta shafa, wanda ya haifar da tarin kayayyakin da aka kiyasta nauyinsu ya kai tan 180.
NCAA ta ce tana ci gaba da bibiyar lamarin domin ganin an dawo da sauran kayayyakin fasinjojin Najeriya, yayin da ake neman warware matsalar da ta haifar da jinkirin jigilar kayayyakin daga Saudiyya.
