Gwamnatin Kano ta sha alwashin ci gaba da gudanar da harkokin mulkinta a bude yadda kowane dan jihar zai san me yake faruwa, a bangaren inganta gaskiyar tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, yaƙi da cin hanci da rashawa, sauyin yanayi, inganta ayyukan gwamnati da kuma ƙarfafa shigar al’umma cikin tafiyar da mulki.
Babban mai taimakawa gwamna Abba Kabir Yusif kan shirin gudanar da mulki a bude Musaddiq Kabir Adam ne ya bayyana hakan lokacin da wakilan ƙungiyoyin fararen hula da ke cikin shirin na mulkin Kano a bude suke zaben shugabannin su.
Musaddiq ya ce shirin tuni ya samar da sauye-sauye a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Kano, tare da ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a fannonin noma, albarkatun ruwa, ilimi da lafiya domin inganta ayyukan gwamnati, wanda hakan duka suna samuwa ne da ra’ayin al’ummar jihar.
Shi ma a nasa jawabin a wajen zaben, mai baiwa shugaban kungiyar ta kasa shawara kan harkokin ƙungiyoyin fararen hula, Jonathan Asake, wanda Sfiyanu Lawan Bichi yayi jawabi a madadin sa, ya ce ayyukan kungiyar ta su ya dace da manufofin gudanar da mulki a bude na duniya, tare da yabawa Gwamnatin Kano bisa rungumar tsarin da shigo da al’umma a mulkin ta.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa kungiyar ta zabi Alhaji Abdulrahman Abdul a matsayin shugabanta na Kano, yayin da gwamnatin kano ta zabi kwamishinan ma’aikatar bibiyar ayyukanta Iro ma’aji Sumaila domin ya wakilce ta, inda zasu yi aiki kafada da kafada domin ciyar da jihar gaba.
