
Ishaq Sani Dambazau
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniya da Iran wadda za ta hana ƙasar samar da makamin nukiliya, tare da tabbatar da sake buɗe mashigar Hormuz a yau Lahadi.
Sai dai wannan saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya zo ne bayan kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya nuna har yanzu babu lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar.
Wakilin BBC ya ce Iran ta fi nuna takatsantsan kan lokacin sanya hannun, watakila saboda har yanzu basu daddale kan batun ba.
Jiya Asabar ita ma Pakistan, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen sasanta ɓangarorin, ta ce ana sa ran kammala yarjejeniyar cikin sa’o’i 24 masu zuwa, tare da bayyana cewa ana shirye-shiryen sanya hannu ta Internet.
