Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai suna Samuel Ogochukwu, wanda aka ce an taɓa yanke wa hukunci kan safarar miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, rundunar ta ce ta ceto wani yaro mai shekaru 14 da ake zargin ana amfani da shi wajen kai saƙon miyagun ƙwayoyi.
Sai dai hukumar bata yi ƙarin bayani kan yadda aka gudanar da kamen ko halin da ake ciki game da binciken ba.
