Daga Safina Abdullahi Hassan
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kaddamar da fara aikin gina hanyar jirgin kasa da zai zagaye birnin Maiduguri.
Wannan aiki shi ne irinsa na farko da wata gwamnati daga cikin gwamnatocin jihohin arewa 19 ta kaddamar.
Kashin farko na aikin zai fara ne da gina tashoshin jirgin kasa 12 a birnin Maiduguri, wanda zai karade manyan kasuwanni da makarantu da wuraren taron jama’a da na harkokin tattalin arziki.
Za a iya fadada aikin yadda zai kai dukkan yankunan kananan hukumomin jihar Borno a nan gaba.
Haka kuma aikin zai taimaka wajen saukaka jigilar fasinja da kayayyaki tare da bunkasa hada-hadar tattalin arzikin yankunan jihar.
Kwamishinan Ayyuka na jihar Aliyu Muhammad Bamanga ya je rangadin duba tashoshi da hanyoyin farko da aka tsara na aikin jirgin kasar tare da kamfanin gine-gine na EEC,
“Ana nazarin wuraren da aikin zai bi, tare da auna matsalolin zai iya yi wa muhalli. Muna tuntubar al’ummar da aikin zai bi ta yankinsu domin tabbatar da nasarar aiwatar da shi”. Inji shi
Alummar jihar borno kuwa sai San barka suke da farun wannan abu na tarihi kuma na farko arewa.