Gwamnatin Jihar Kebbi ta kafa wani kwamitin musamman domin gudunar da bincike kan gobarar da aka samu a wasu makarantun jihar.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da Sakataren Yada Labaran Gwamnan jihar ta Kebbi, Yahaya Sarki, ya fitar a ranar Alhamis din data gabata.
Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan Ma’aikatar Fasaha da Bunkasa Tattalin Arzikin na Zamani, Alhaji Ibrahim Muhammad Sakaba, shi ne zai jagoranci kwamitin, hadin gwiwa da Shugaban Hukumar ilimin bai daya na jihar wato SUBEB, Farfesa Sulaiman Khalid da babban sakataren Ma’aikatar Ilimi, da wakilan hukumomin tsaro da suka hada da ’yan sanda, DSS da Hukumar da kuma na Kashe Gobara.
- Tinubu ya buƙaci jami’an tsaro su killace dazukan jihohin Kwara,Kebbi, Neja
- Za Mu Dauki Dukkan Matakai Don Ceto Daliban Kebbi – Gwamnatin Tarayya
- Atiku ya soki gwamnati tarayya kan yadda aka saki daliban jihar Kebbi
An dora wa kwamitin alhakin binciken dalilan tashin gobarar tare da tantance irin asarar da aka yi, da kuma bayar da shawarwari kan matakan tsaro da kuma kariya domin hana sake faruwar lamarin a nan gaba.
Gwamnatin jihar ta ce za ta duba rahoton kwamitin tare da shawarwarin da ke cikinsa domin daukar matakan kare dalibai, malamai da kuma makarantu jihar ta Kebbi.
