Jam’iyyar APC ta ce manyan ‘yan adawa da ke cikin ADC, ciki har da Atiku Abubakar, ba su da wani tasiri a siyasance duk da irin kwarewar da suke da ita.
Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ne ya bayyana hakan a hirarsa da gidan Talabijin na Channels inda ya ce ba su da wani tasiri a siyasa.
Morka ya ambaci cewa duk da cewa Atiku ya taba zama mataimakin shugaban ƙasa, Rotimi Amaechi ya taba zama gwamna da minista, sannan Rauf Aregbesola ya rike mukamai daban-daban, amma haɗuwarsu a ADC bai haifar da wani gagarumin sauyi ba.
Ya kuma ƙalubalanci ADC da ta gabatar da hujjoji kan zargin da take yi wa APC na tsoma baki a rikicin cikin gida na jam’iyyar, yana mai cewa APC ba ta da dalilin tsoron ADC.
