Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ne ya jagoranci wata yarjejeniya tsakaninsu da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bayan zaɓen 2023, wadda ta tanadi komawarsu jam’iyyar APC idan har shugaban ƙasar bai tsoma baki a shari’ar zaɓen gwamnan Kano ba.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, karon farko tun bayan sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Gwamnan ya ce bayan zaɓen 2023 ne suka gana da Shugaba Tinubu, inda suka yi yarjejeniya cewa idan bai tsoma baki a shari’ar da ke ƙalubalantar nasarar da ya samu kan ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna ba, za su koma jam’iyyar APC.
Ya ƙara da cewa daga baya Sanata Kwankwaso ya yi watsi da yarjejeniyar, duk da cewa shi ne ya buƙaci a tabbatar da ita har da yin rantsuwa a kan Alƙur’ani.
A cewar Abba, Kwankwaso ne da kansa ya tura shi wajen Tinubu domin ya tabbatar masa da wannan alƙawari, yana mai cewa an kuma buƙaci ya yi rantsuwa da Alƙur’ani idan hakan ya zama dole, domin tabbatar da aniyar komawa jam’iyyar APC idan suka samu nasara a shari’ar.
