Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci iyaye, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki a jihar da su haɗa ƙarfi wajen yaƙi da zaman banza, gurɓacewar ɗabi’u da tarbiyya da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa.
Gwamnan ya yi kiran ne yayin ziyarar da ya kai wasu wuraren Mauludi guda 8 a birnin Kano, waɗanda aka shirya domin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Gwamna Abba ya nuna damuwa kan yadda wasu miyagun halaye ke ƙara yaɗuwa tsakanin matasa, irin su satar waya, faɗan daba, shaye-shayen ƙwayoyi da ɓata sunan mutane a kafafen sadarwar zamani.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya ce akwai buƙatar dukkan masu ruwa da tsaki, musamman malaman addini, su haɗa hannu wajen dakile matsalar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnanna buƙatar iyaye da su ƙara ƙaimi wajen tarbiyyar ’ya’yansu bisa kyawawan ɗabi’u, yayin da ya roƙi malaman addini da su ƙara wa’azi da addu’o’i domin samun mafita daga matsalolin da ke addabar matasa.
