Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta haramta digirin da ake samu ta hanyar jami’o’in karatu daga gida wato (Online Universities) ba, sai dai ta jaddada muhimmancin tabbatar da inganci da sahihancin cibiyoyin da ke bayar da irin wannan karatu.
Ƙaramar ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce abin da gwamnati ta dakatar shi ne amincewa da takardun shaidar wasu jami’o’in ƙasashen waje da ba su cika ƙa’idojin da suka dace ba, ba wai dukkan jami’o’in karatu ta intanet ba.
Ta ce abinda gwamnati tafi mayar da hankali a kai shine tabbatar da cewa makarantun da ke bayar da irin waɗannan karatu suna da sahalewa da kuma cika ƙa’idojin da hukumomin da suka dace suka gindaya.
ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ta yi da kafar yaɗa labarai ta DCL, inda ta ce tsarin karatun yanar gizo na daga cikin hanyoyin ilimi da ake amfani da shi a sassa daban-daban na duniya
Farfesa Suwaiba Ahmad ta kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ingancin ilimi, tare da ƙarfafa hanyoyin koyarwa na zamani da za su taimaka wajen bunƙasa ilimi a ƙasar nan.
